Amurka ta ƙaƙaba wa shugaban Zimbabwe sabbin takunkumai
Amurka ta ƙaƙaba wa shugaban Zimbabwe sabbin takunkumai
Amurka ta sanya sabbin takunkumai a kan sugaban ƙasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa kan cin hanci da take haƙƙin ɗan'adam.
Sabbin takunkuman sun kuma haɗa da wasu manyan jami'an gwamnatin ƙasar - waɗanda ta hana taɓa kadarorinsu da ke Amurkar tare da hana zu kai ziyarar ƙashin kansu ƙasar.
Sabbin takunkuman sun maye gurbin waɗanda aka sanya wa ƙasar ta Zimbabwe kimanin shekara 20 da suka wuce.
"Muna ci gaba da ganin yadda ake keta haddin ƴansiyasa da wasu haddin da suka shafi tattalin arziki da na bil'adama." A cewar wata sanarwa ta fadar White House.
"Ana harin ƙungiyoyin fararen hula tare da hana ƴansiyasa sakat, ta hanyar take muhimman haƙƙoƙinsu na walwala, yayin da manyan jami'an gwamnati ke ci-gaba da sace kuɗaɗe daga lalitar gwamnati don amfanin kansu," a cewar sanarwar.
"Munanan ayyukansu na taimakawa tare da tallafawa manyan gungun masu aikata manyan laifukan cin hanci na duniya, fasakwauri, halalta kuɗin haram da ke ƙara jefa al'umomin Zimbabwe da kudancin Afrika da wasu sassan duniya. "